Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Tambayoyi da amsarsu tare da Mallam Ibrahim Zakzaky na goma sha biyu

Sayyed Zakzaky2

Ana iya ba Yara Bammi don maganin Kyanda?

Mai karatu a ranar Talatar da ta gabata muka sami zama da Shaikh Zakzaky, ya kuma amsa wasu tambayoyinku. Mun dan dade Malam na ta amsa tambayoyi. Muna godiya ga Malam kan haka. Muna sa ran za mu kwana biyu muna bugo muku, kafin mu sake samun wani lokacin tare da Malam. Don haka masu tambayoyi da sauran masu biye da filin nan sai mu ce su biyo mu sannu a hankali. Muna kara yi wa masu aiko da tambayoyin tuni cewa su rika yin tambaya mai ma'ana. Don duk tambayar da ba ta da ma'ana, ko muka kasa gane abin da mai tambayar ke so a amsa masa, za ta shiga kwandon shara. A sha karatu lafiya.




TAMBAYA: Assalamu alaikum. Ni ne na yi alkawari zan taimaki makarantar Fudiyya da kudi Naira 200, kowane wata, amma na yi watanni 30 ban ba da ba, zan ba da rabin abin da na yi furuci da farko ne, ko zan biya gaba daya ne?

Daga Muhammad Bawa Takalau

SHAIKH ZAKZAKY: Alkawari dai wajibi ne mutum ya cika shi, musamman idan ya hada shi da alwashi. Idan ya aje shi da alwashi zai zama kaffara ya hau kansa. Amma tunda alkawari ne, za mu dauka ba tare da alwashi bane, saboda haka babu batun kaffara. Amma abin da ya hau kansa, tamkar bashi. Abin nan da ya ce zai rika biya duk wata, to ko da ya kwashe wata nawa ne bai biya ba, jimlarsa yana kansa.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Sana'ata wanki da guga, menene hukuncin kayan da masu kawo wanki suka bar ni da su? Don akwai kayan mutanen da suka shekara biyar ko sama da haka a wajena.

Daga Idris Salihu Marabar Jos jihar Kaduna

SHAIKH ZAKZAKY: To hukuncinsu zai koma tamkar hukuncin kayan tsintuwa, kodayake su wannan an ba shi ne amana, amma bai san wanene ya ba shi ba. Sai ya yi ta bincike, ya yi ta bincike, har sai ya gano wanene ya ba shi din. Kuma matsawar bai gano ba, zai ta ajiyewa, tunda amana ce. Inda ya bambanta da tsintuwa kenan. Tsintuwa ba ka san mai shi ba dama, shi kuwa wannan ka san wani ya ba ka. Saboda haka sai ka ajiye daidai gwargwadon shekara guda, idan ka tabbatar da cewa ba ka gane mai shi ba, to shi kenan kana iya sarrafa shi ta fuskar duk da ka so, amma kai ne mai lamuni. Fuskokin ya hada da ko ka bayar sadaka, ko ka sayar ka dauki kudin ka yi sadaka da fatan ladan ya je ga shi mai kayan. Amma duk ran da mai kayan ya zo, to lazim ne ka biya shi. Ba za ka ce ai na yi maka sadaka da shi ba.

Amma idan ya san takamaimen mai shi (wannan idan na fahimci maganar bai fahimci waye mai kayan ba),sai ya zama mai kayan ya tashi ya tafi wani wuri, to ko shekara nawa ya yi ba zai salwantar da kayan ba, zai ajiye masa, tunda ya koma tamkar hukuncin ajiya, ba na tsintuwa ba. Idan mutum ya ba ka ajiya, za ka yi ta ajiyarsa, sai dai in an kai ga wannan abin zai salwanta, ya lalace sakamakon ajiya, to ba za ka bar shi ya lalace ba, saboda haka sai ka sayar da shi ko ka sarrafa shi ta wata hanya don ya zama kiyayewa gare shi, kudin kuma zai zama na wannan mutumin ne. Duk lokacin da ya dawo sai ka ce masa ka bar kayanka, bayan shekara kaza muka ga alamar zai lalace, saboda haka mun sayar.

Idan kuma ya yaye masa cewa mai kayan misali ya mutu ne, to na magadansa ne. Sai ya kai wa magadan kayan. Idan kuma ya san wadanda suke da dangantaka da mutumin, in ba shi nan ko da ma ya bace ne, yana iya kai musu.

TAMBAYA: Akramakallahu. Menene bambanci tsakanin Mahr da Sadak

Daga Bello Dogara Mai gyaran agogo Bomo, Zariya

SHAIKH ZAKZAKY: Akwai luggogi na sadaki a Larabci, amma a Hausa ba mu da mishkila a kan wannan, saboda sadakin kawai muke ce masa. Ba ma kiran shi da wani suna, akalla a addinance. A al'adance akwai abubuwan da suke ce masu ko dukiyar aure, kayan asin da asin, ko toshi, wadanda duk ba su a cikin ma'anar sadaki.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Wace addu'a ake karantawa don fid da aljannu daga jiki ta bangaren Iyalan gidan Manzo(S)?

Daga Bello Dogara Mai gyaran agogo Bomo Zariya

SHAIKH ZAKZAKY: Irin wadannan ruwayoyin suna da yawa. Mutum zai iya duba su a mahallansu, musamman littattafai ma'asurai na addu'a, wadanda ga su nan latu'addu wala tuhsa. Zai ga wadansu wadanda aka ruwaito. Akwai ma wadda Manzon Allah ya taba ba shi wata wasika, ya ce ya je ya aje a dakin. Kuma har ya ji su suna kururuwa, suna cewa ya dauke musu wannan wasikar. A ciki Manzon Allah ya ce wannan daga Manzon Allah ne zuwa ga aljanun da suke wurin a kan cewa su fita. Sai dai muhallinsa ya kamata ya nema, ya samu a cikin littattafan addu'o'i ma'asurai.

TAMBAYA: Akramakallahu. Mutum ne Direban mota, sai ya yi hatsari, mutane 50 suka mutu, kuma ba tukin ganganci ya yi ba. To menene sakamakon wannan mutumin. Kuma idan shi ma ya rasa ransa, to hukuncin kan wa ya hau kenan? Kuma wasu direbobin kan buge mutum har ya rasa ransa, amma sai a ce an yafe masu, shin wannan ya halasta?

Daga Muhammad Awwal 'yankara Jaula

SHAIKH ZAKZAKY: Tunda ya ce ba na ganganci bane, wato kenan hadari ne ya auku, ba sakamakon sakacin direba ba, to zai zama kenan ba abin da ya hau kansa. Amma da a ce sanadiyyar hadarin sakaci ne daga nasa bangaren, to ko da mutum hamsin ne ko fiye to yana daidai da hukuncin wanda ya kashe su bisa kuskure. Kuma zai hau kansa ya biya diyyarsu, ya kuma yi kaffara. A kaffarar, na azumi tunda ba zai yiwu ba, sai a koma ga ciyarwa. Kuma idan mutumin ya tabbata ya yi ganganci, har kuma ya zama sanadiyyar rasuwarsa shi a kan kansa da kashe wasu, to shi dangane da rasuwarsa shi ya kashe kansa kenan, amma sauran zai koma ga magadansa. Sune alhakin biyan diyya ya hau kansu. Tunda shi yake kaffara kuma ya mutu, to shi kenan wannan ya fadi. Sai dai su yi masa addu'ar Allah ya yafe masa.

Kuma idan ma'abota hakki na diyya suka ce sun yafe, to shi kenan ya halasta, ya yafu.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Akwai ruwan wani itace a kudancin kasar nan wanda ake kira bammi, ana sha, kuma yana bugarwa kamar giya. Amma a nan Arewa ana ba yara in suna yin kyanda, kuma suna warkewa, to menene hukuncinsa a wajen yaran?

Daga Muhammad Awwal 'yankara Jaula Photos

SHAIKH ZAKZAKY: Ba a magani da giya, sai idan ya zama dole. Saboda haka sai a nemi wani magani ba wannan ba. Giya kuma, in dai abu na bugarwa sunansa giya, komai karantarsa, in dai mai yawansa zai bugar, kadan din sa ma wanda ba zai bugar ba ya haramta. Hatta in da ma za a surka shi da ruwa, ya zama giyan dan kadan ne, duk da haka zai haramta. Saboda haka ana magani da giya kawai in ya zama dole ne. In ya zama ba a san wani magani ba illa wannan, zai zama babu laifi da shi gwargwadon da ba zai iya bugarwa ba ko a sha ko a shafawa.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Idan aka soya ko aka dafa kifi wanda ya halasta a ci da wanda bai halasta a ci ba tare, ya halatta mutum ya ci wanda ya halatta a ci, ko ya sha miyar ko kuwa gaba daya bai halatta mutum ya ci ko ya sha miyar ba?

Daga Umar mai walda, Gashuwa

SHAIKH ZAKZAKY: Abin da ya haramta a ci bai kamata har wala yau ya zama an sha ruwansa ba, don shi ma ruwan bangare ne nasa. Sai dai dangane da sha'anin su nama, tana iya yiwuwa a dafa wani bangare wanda yake shi an hana ci. Kamar nama, bangaren da ba a ci, to ana iya hada shi da wanda ake ci a dafa, amma in an zo a fid da shi. Kamar misali mu kaddara ka sai balangu, ya zama da saifa, to in ka tsittsince saifar ka zubar ba laifi. Haka zalika kashi, kodayake shi kashi akwai sabani. Wasu suna haramtawa, wasu sun ce in ya inganta ba ya cutarwa ana iya ci, to shi ma za a iya tsotsewa a yar. Wannan dangane da nama ne. Amma in aka ce wannan kifi ne wanda ya haramta a ci, to shi ba za a saka shi a cikin miya a dafa shi ba, tunda shi ma kamar an ci shi ne. Haka zalika nau'o'in nama na abin da aka haramta a ci, kamar misali gafiya, wadda take haramun ce, a hada ta da naman kaza. Ba zai halatta ba.

.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din


XtGem Forum catalog